ABNA24 : Masu jerin gwanon sun daga tutocin Palasdinu sannan kuma su ka kona tutar HKI suna masu bayar da taken ‘mutuwa ga Amurka da Isra’ila”
A can kasar Iraki ma an gudanar da gangami da kuma jerin gwago na raya ranar ta Kudus, a cikin birane da dama. Daga birnin Bagadaza, zuwa Basra da Zi-qar da Nasiriyyah, duk an gudanar da jerin gwanon na ranar Kudus.
A can ma kasar Bahrain an yi jerin gwano a cikin biranen kasar mabanbanta tare da bayar da taken nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu.
A wasu kasashen nahiyar Afirka ma an gudanar da irin wannan jerin gwano da kuma taruka na na musammana domin raya wanann rana, daga ciki har da Kenya da kuma Tanzania, Afirka ta kudu da Ghana, mali, Senegal.
A Najeriya kuwa an gudanar da taruka daban-daban kuma jerin gwano a birane daban-daban, domin raya wannan rana ta Quds ta duniya.
342/